Madugun 'yan tawayen Sudan ta kudu ya shelanta yaki a kasar
Tsohon mataimakin Shugaban kasar Sudan ta kudu ya ce yarjejjeniyar sulhun da suka cimma da Gwamnati ba ta da wani tasiri.
Kamfanin dillancin labaran kasar Faransa ya habarta cewa tsohon mataimakin shugaban kasar Sudan ta kudu kuma madugun 'yan tawaye Riek Machar cikin wani bayyani da ya fitar a wannan lahadi ya shelanta yaki da Gwamnatin kasar inda ya ce a halin da ake ciki yarjejjeniyar sulhun da aka cimma tare da taimakon kungiyoyin kasa da kasa ba ta da wani tasiri a halin da ake ciki.
Riek Machar ya yi wannan kira ne daga birnin Khartum na kasar Sudan, inda ya ce wajibi ne su yi gwagwarmaya domin samawa kasar 'yanci da kuma tsarin Demokaradiya.
A shekarar 2011ne kasar Sudan ta kudun ta samu 'yan kai daga kasar Sudan, amma tun kafin aje ko ina a watan Decembar 2013 kasar ta fara cikin yakin basasa sanadiyar rikicin mikami, a karshen shekarar 2015 an kawo karshen rikici bayan cimma yarjejjeniyar sulhu tsakanin Gwamnati da kuma 'yan tawayen kasar to saidai a 'yan watanin da suka gabata rikici ya sake kunno kai tsakanin Sojojin dake biyayya da Gwamnati da kuma na mataimakin shugaban kasa na farko kuma tsohon madugun 'yan tawayen kasar bayan da shi kansa Shugaban kasar Salva keir ya yi kokarin kama mataimakin na sa na farko Riek Machar