Tsagerun Niger-Delta sun galgadin Gwamnatin Najeriya
Tsagerun Niger-Delta sun bayyana cewa na da 'yan kwanaki masu zuwa za su kaddamar da munanan hare-hare kan kamfanonin Man na kasashen waje a yankunan kudancin Najeriya
Kafar watsa labaran Afirka News ta nakalto Tsagerun Niger-Delta Avengence cikin wata sanarwa da suka fitar a wannan lahadi,sun galgadi Gwamatin Najeriya kan rashin kulawa da ta yi na bukatunsu, sannan suka ce ba za su bari Gwamnatin ta ci gaba da yin kunan uwar sheku dangane da bukatun da suka gabatar mana don hakan nan da 'yan kwanaki masu zuwa a saurari martani da za su mayar domin sun shirya ci gaba da kai munanan hare- hare kan cibiyoyi da kumafanonin Man fetur din kasar da na 'yan kasashen wajen a kudancin kasar.
Wannan sanarwa na zuwa ne a yayin da Majiyar tsaron Najeriya ta sanar da gano tare da cabke Ibrahim Souro shugaban kungiyar ta Niger-Delta Avangence a yankin.
A watan da ya gabata ne Kungiyar tsagerun Niger-Delta Avengence ta bayyana cewa ta dakatar da hare-haren da take kaiwa kan bututun Man kasar,Tun daga farkon wannan shekara, Gwamnatin Najeriya ta fara fuskntar fashe-fashen bututun Man fetun daga tsagerun Niger-Delta Avengence, lamarin da ya yi sanadiyar raguwar danyan man da kasar ke fitar wa a ko wata rana, da kimanin ganga dubu 700, inda Gwamnati ta dawo tana fitar da ganga million daya da dubu 560a ko wata rana.