An karyata labarin raunana shugaban kungiyar Boko Haram
Kungiyar Boko Haram ta fitar da wani sabon hoton bidiyo, a inda sa Shugaban kungiyar Abubakar Shekau ya karyata sojojin Najeriya cewa sun raunata shi.
A cikin sabon bidiyon wanda kungiyar ta fitara wannan safiya ta Lahadi, Abubakar Shekau ya kwashe kimanin minti 40 yana magana da harsunan Hausa da Larabaci da kuma Kanuri.
Da farko Shekau ya karyata Rundunar sojin Najeriyakan labarin da ta basyar na cewa ta jikkata shi a wani harin sama da ta ce ta kai kan 'yan Boko Haram, sannan ya tabbatar da cewa yana cikin koshin lafiya babu abinda ya same shi.
Baya hakan, Abubakar Shekau ya bayyana Najeriya da kasar kafirci, a inda ya rera taken Najeriya da Turanci, sannan ya bayyana shi da wata alama ta kafirci.sannan ya ce za su ci gaba da kai hare-hare a Najeriya, har zuwa lokacin da kasar za ta koma kan tafarki irin nasu.
kimanin Shekaru bakwai kenan da kasar Najeriya ke fuskantar hare-haren ta'addanci na kungiyar Boko Harm a shiyar arewa maso gabashin kasar, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane kimanin dubun 20 sannan kuma ya raba wasu kimanin million biyu da dubu 600 da gidajen su.