Shugaban Kasar Gabon Zai Saba Layar Fara Zango Na Biyu Na Shugabaci
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i11611-shugaban_kasar_gabon_zai_saba_layar_fara_zango_na_biyu_na_shugabaci
Ali Bango zai yi rantsuwar kama aiki na zango na biyu a shugabancinsa wanda zai dauke shi shekaru bakwai.
(last modified 2019-04-27T09:55:10+00:00 )
Sep 26, 2016 15:35 UTC
  • Shugaban Kasar Gabon Zai Saba Layar Fara Zango Na Biyu Na Shugabaci

Ali Bango zai yi rantsuwar kama aiki na zango na biyu a shugabancinsa wanda zai dauke shi shekaru bakwai.

Ofishin shugaban kasar ta Gabon ya sanar a yau litinin cewa; a gobe talata ne shugaban kasar Ali Umar Bango zai saba layar kama aiki, bayan da kotun kolin kasar ta tabbatar da ingancin zaben da aka yi.

Sanarwar ta ci gaba da cewa:

 Kotun kolin kasar ta Gabon dai da ta tabbtar da ingancin zaben, ta kuma yi watsi da karar da  dan takarar shugabancin kasar, Jean Ping ta shigar a gabanta na bukatar a sake kirga kuri'u.