An Kashe 'yan ta'addar al-shabab biyu a kasar Somaliya
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i11617-an_kashe_'yan_ta'addar_al_shabab_biyu_a_kasar_somaliya
Dakarun Afirka Sun kashe 'yan al-shabab biyu
(last modified 2018-08-22T06:58:59+00:00 )
Sep 26, 2016 15:46 UTC
  • An Kashe 'yan ta'addar al-shabab biyu a kasar Somaliya

Dakarun Afirka Sun kashe 'yan al-shabab biyu

Dakarun tabbatar da tsaro na kasashen Afirka da ake kira       ( Amsiom) sun kashe 'yan kungiyar al-shabab biyu a garin Kimaeo da ke kudancin kasar Somaliya.

Kamfanin dillancin Labarun Xinhua na kasar Sin ya nakalto cewa; kashe 'yan al-shabab din biyu ya biyo bayan gumurzun da aka yi ne a jiya lahadi wanda ya ci rayukan mutane 10.

Majiyar dakarun ta ( Amsiom) ta ce sun kashe 'yan kungiyar ta al-shabab biyu ne a lokacin da su ke share garin kimaeo da ke gabar ruwa daga 'yan ta'adda.

Rashin tsaro da ake fama a kasar ta Somaliya ya sa an dage zaben 'yan majalisa da aka shirya yi a ranar asabar din da ta gabata.