An Sanar Da Dage Ranakun Zabe A Kasar Somaliya Saboda Matsalar Tsaro
Hukumar zaben kasar Somaliyya ta sanar da jinkirta lokacin gudanar da zabubbukan shugaban kasa da na 'yan majalisar kasar da aka shirya gudanarwa a watan Oktoban nan mai kamawa zuwa watan Nuwamba mai zuwa saboda matsalar tsaro da ake fuskanta a kasar.
Kamfanin dillancin labaran kasar Faransa ya bayyana cewar a cikin wata sanarwa da hukumar zaben ta sanar ta ce an dage lokacin gudanar da zaben 'yan majalisar kasar da aka shirya gudanarwa a ranar 23 ga watan Oktoba zuwa ranar 10 ga watan Nuwamba, sannan zaben shugaban kasa kuma za a gudanar da shi kafin 30 ga watan Nuwamban.
Sanarwar ta kara da cewa duk da gagarumin aikin da aka yi wajen ganin an gudanar da zaben a kan lokaci, to amma sakamakon wasu matsaloli da suka kunno kai cikin kuwa har da matsalar tsaro don haka ya zama dole a dage lokacin gudanar da zaben don samun karin lokacin gudanar da sauran ayyukan da suka sauran.
Wannan dai ba shi ne karon farko da aka dage lokacin gudanar da zaben ba sakamakon matsalar tsaron da kasar take fuskanta bugu da kari kuma kan matsaloli na siyasa da suka kunno kai lamarin da ya sanya kungiyar Tarayyar Afirka kiran 'yan siyasar kasar zuwa ga aiki tare wajen ganin an share fagen da tsarin demokradiyya zai gudana a kasar.