Shelanta yaki kan Gwamnatin Sudan ta Kudu.
Tsohon mataimakin Shugaban kasar Sudan ta Kudu ya shelanta yaki da Gwamnati.
A ranar lahadin da ta gabata, tsohon shugaban kasar Sudan ta kudu Riek Machar ya shelanta yaki da Gwamnatin kasar inda ya ce a halin da ake ciki, yarjejjeniyar sulhun da suka cimma tare da Gwamnati ba ta da wani tasiri domin Gwamnatin Salva Keir ta yi watsi da ita.Riek Machar ya bayyana haka ne daga birnin Khartum fadar milkin kasar Sudan, inda a can ne ya samu mafuka tun bayan da ya tsare daga cikin kasar sa a watan Yunin da ya gabata, bayan da wani sabon rikicin ya sake barkewa a kasar,Mashar ya bayyana shirin sa na gwagawarmaya da nufin dawo da sulhu,tafarkin Demokaradiya tare da 'yanci a kasar Sudan ta Kudu.
Wannan sanarwa ta Tsohon Shugaban kasar sudan ta Kudu na zuwa ne maku guda bayan da Gwamnatin ta bayyana fatanta na zartar da yarjejjeniyar sulhu a matsayin matakin tabbatar da sulhu gami da zaman lafiya a kasar.a cewar James Wani Igga mataimakin Shugaban kasar Sudan ta Kudu, Gwamnati na iya kokari wajen dawo da sulhu gami da konciyar hankali matukar dai ta samu goyon bayan Al'ummar kasar tare da zartar da yarjejjeniyar sulhu da aka cimma tare da masu tayar da kayar baya.sannan ya bukaci Al'ummar kasar da su zamanto masu taka tsantsan wajen kula da Al'amura kada su yarda a yaudare su wajen rura wutar fitina a kasar.
Bayan kwashe watani ana gwabzawa fada tsakanin Sojoji masu biyayya da Gwamnatin Salva keir da kuma bangaren masu biyayya da tsohon mataimakin Shugaban kasar na farko Riek Machar, a karshen shekarar da ta gabata, an cimma yarjejjeniyar sulhu tsakanin bangarorin biyu, lamarin da ya sanya fata a zukatan Al'ummar kasar wajen dawo da konciyar hankali, to saidai tun daga wannan lokaci wasu kwararu kan harakokin siyasar kasar suka bayyana shakkun su dangane da dorewar wannan yarjejjeniya.mayuwacin halin da Al'ummar kasar suka shiga na yunwa da talauci da kuma tsoron kakabawa kasar takunkumi na daga cikin ababen da suka sanya bangarorin biyu zartar da yarjejjeniyar sulhun, bayan raba mikamai tsakanin bangaren Gwamnati da na Mataimakin tsohon shugaban kasar kuma tsohon madugun 'yan tawayen Riek Machar, mafi yawa daga cikin Al'ummar kasar da kuma kungiyoyin kasa da kasa gami da kasashen yankin sun bayyana fatan su na kawo karshen tashin hankali a kasar.to saidai barkewar sabon rikicin da yayi sanadiyar mutuwar Sojoji da dama tare da yin gudun hijra na 'yan kasar masu yawa ya canza duk wani fata da Al'ummar kasar ke da shi. bayan ficewar Riek Machar daga cikin kasar da kuma nada sabon mataimakin Shugaban kasar na farko daga cikin magoya bayansa, Gwamnatin Shugaba Salva keir ta bayyana fatanta na sake dawo da sulhu a cikin kasar inda a makun da ya gabata, Ministan tsaron kasar Kuol Manyang Juuk da kuma Akuei Bona Malwal wakilin kasar a MDD suka ce a halin da ake ciki zaman lafiya ya fara dawowa cikin kasar har ma Majalisar Dokokin kasar ta fara gudanar da aiyukanta.
A halin da ake ciki matukar dai mabiyar Riek Macahr din suka bi umarninsa to shakka babu kasar na iya sake fadawa cikin rikici da kuma zubar da jini, to saidai masu shiga tsakani na kasashen yankin sun bukaci bangarorin biyu da su sake zama kan tebirin shawara domin hana sake barkewar yaki a kasar.