Muhimmancin Tattaunawa Tsakanin Gwamnatin Suda Da 'Yan hammayya A cikin Gida.
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i11674-muhimmancin_tattaunawa_tsakanin_gwamnatin_suda_da_'yan_hammayya_a_cikin_gida.
Shugaban Kasar Sudan, ya jaddada muhimmancin Tattaunawa Da 'Yan hamayya A cikin Gida.
(last modified 2018-08-22T06:59:00+00:00 )
Sep 28, 2016 03:48 UTC
  • Muhimmancin Tattaunawa Tsakanin Gwamnatin Suda Da 'Yan hammayya A cikin Gida.

Shugaban Kasar Sudan, ya jaddada muhimmancin Tattaunawa Da 'Yan hamayya A cikin Gida.

Kamfanin Dillancin Labarun Xiunhua na kasar Sin, ya ambato shugaba Umar Hassan al-Bashir na Sudan yana  yin kira ga 'yan hamayya a jiya talata, da a ci gaba da tattaunawar sulhu a cikin gida, ba a waje ba.

Shugaban na kasar Sudan ya kuma ce gwamnati tana son ganin an cimma matsaya ne wacce za ta kare manufofin dukkanin bangarorin biyu.

A ranar 10 ga watan Oktoba ne za a bude wani zango na tattaunawa a tsakanin gwamnati da kuma 'yan hamayyar kasar a birnin Khartum.

Tattaunawar dai ana yinta ne a tsakanin gwamnatin Khartum da kuma 'yan hamayyar daga yankunan Darfur da Blue Nile da Kurdufan ta kudu.