Ana ci gaba da Kashe Mutane A Kasar Afirka Ta Tsakiya
Majalisar Dinkin Dunkiya ta Sanar da mutuwar mutane da yawa a Afrika ta tsakiya
Kafar watsa labaru ta "Africa Time" ta ambato kakakin dakarun tabbatar da zaman lafiya na majalisar dinkin duniya a Afirka ta tsakiya, Vladimir Monteiro, yana cewa; A tsakiyar watan Satumba an sami mutuwar mutane tsakanin 10 zuwa 20 a garin Kouango da ke tsakiyar kasar.
Vladimir Monteiro ya kara da cewa 'yan tawayen Seleka ne masu tada hargitsi a kauyen na Kouango, kuma suna ci gaba da kashe fararen hula da kona gidane a cikin wasu kauyuka.
Kakakin dakarun tabbatar da zaman lafiyar na majalisar dinkin duniyar ya kara da cewa; Da akwai dakaru 12,000 da su ke aiki da gwamnatin kasar ta Afirka ta tsakiya, a fadin kasar.
A shekarar 2013 ne kasar ta Afirka ta tsakiya ta fada rikicin kabilanci da addini wanda ya ci rayuka da dama.