Jiragen yakin Amurka sun kai hare-hare a kasar Somaliya
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i11704-jiragen_yakin_amurka_sun_kai_hare_hare_a_kasar_somaliya
Ma'aikatar tsaron Amurka Pentagon ta sanar da kashe mayakan kungiyar Ashabab 9 a wani hare-hare da jiragen yakin ta suka kai a Somaliya
(last modified 2018-08-22T06:59:00+00:00 )
Sep 29, 2016 02:15 UTC
  • Jiragen yakin Amurka sun kai hare-hare a kasar Somaliya

Ma'aikatar tsaron Amurka Pentagon ta sanar da kashe mayakan kungiyar Ashabab 9 a wani hare-hare da jiragen yakin ta suka kai a Somaliya

A cikin wata sanarwa da ya fitar da wannan laraba,Kakakin Pentagon Jeff Davis ya ce Dakarun tsaron Amurka tare da na kasar Somaliya yayin da suke kera wani Bam a yankin Puntland sun fuskanci hari daga mayakan kungiyar Ashabab, to saidai bayan wannan hari, Sojojin na Amurka sun kai hari ta sama kan mayakan na kungiyar Ashabab, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane 9.

Sanarwar ta ce a halin da ake ciki ana ci gaba da bincike kan mutanan da aka kashe , mai yiyuwa Mutanan ma  ba mayakan kungiyar Ashabab ne ba.

Mista Davis ya ce babu daya daga cikin Dakarun kasar Amurka da ya rasa ransa ko ya jikkata sanadiyar harin da mayakan Kungiyar Ashabab suka kai musu.

Wannan dai shi ne hari na biyu da Jiragen yakin Amurka suka kai kan mayakan kungiyar Ashabab din a cikin wannan maku da muke ciki.