RDC : Za'a Taimakawa Iyalen Wadandan Suka Mutu A Zanga-Zanga
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i11728-rdc_za'a_taimakawa_iyalen_wadandan_suka_mutu_a_zanga_zanga
Gwamnatin RD. Congo ta ce zata taimakawa iyalen wadanda suka mutu a zanga-zanga baya-bayan nan da $ Amurka 5,000 ko wannensu.
(last modified 2018-08-22T06:59:00+00:00 )
Sep 29, 2016 08:36 UTC
  • RDC : Za'a Taimakawa Iyalen Wadandan Suka Mutu A Zanga-Zanga

Gwamnatin RD. Congo ta ce zata taimakawa iyalen wadanda suka mutu a zanga-zanga baya-bayan nan da $ Amurka 5,000 ko wannensu.

A cewar gwamnatin Kishasa za'a baiwa iyalen duk wani da ya rasa ransa a zanga-zanga da aka fuskanta a kasar a ranarkun 19 zuwa 20 ga watan nan na Satumba.

Ma'aikatar kiwan lafiya ta kasar ce keda nauyin rejistan iyalen tare da kwararen hujjoji, kasancewa tuni aka fara samun rahotanni toge a cikin lamarin.

Saidai babbar jam'iyyar adawa ta kasar ta ce taji takaicin rashin saka magoya bayan ta a cikin wannan tsarin.

Kimanin mutane 49 ne suka rasa rayukansu a borin kin jinin gwamnatin Josef kabila.