Amnesty Ta Zargi Sudan Da Amfani Da Makamai Masu Guba
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i11731-amnesty_ta_zargi_sudan_da_amfani_da_makamai_masu_guba
Kungiyar kare hakkin bil adama ta kasa da kasa Amnesty International, ta zargi sojojin gwamnatin Sudan da hallaka fararen hula da dama ta hanyar amfani da makamai masu guba a yankin Darfur.
(last modified 2018-08-22T06:59:00+00:00 )
Sep 29, 2016 08:36 UTC
  • Amnesty Ta Zargi Sudan Da Amfani Da Makamai Masu Guba

Kungiyar kare hakkin bil adama ta kasa da kasa Amnesty International, ta zargi sojojin gwamnatin Sudan da hallaka fararen hula da dama ta hanyar amfani da makamai masu guba a yankin Darfur.

A rahoton da ta fitar yau Alhamis, Amnesty, ta ce an kai hare-hare kimanin talatin daga watan Janairu zuwa Satumba na wannan shekara da muke ciki a kauyukan dake yankin Djebel Marra, a lokacin da sojojin kasar ke fada da 'yan tawayen. 

Rahoton mai shafukan kusan 100, ya kunshi bayanai daga kwararu da kuma hotinan tauraren kauyukan da aka dauka ta tauraren dan adam da kuma yara kankana da makaman masu guba sukayi wa illah. 

Sudan wace ta rattaba hannu a yarjejeniyar haramta amfani da makamai masu guba tun cikin shekara 1999 ta jima tana bukatar ficewar tawagar MDD ta MUNUAD daga kasar.

Alkalumma daga MDD sun nuna cewa kimanin mutane 300,000 ne suka rasa rayukansu, kana wasu milyan 2,5 sukayi kaura daga gidajensu saboda rikicin na yankin Darfur.