Tsoffin Shugabannin Ghana Sun Bukaci A Gudanar Da Zabe Cikin Kwanciyar Hankali
(last modified Tue, 23 Feb 2016 11:48:19 GMT )
Feb 23, 2016 11:48 UTC
  • Tsoffin Shugabannin Ghana Sun Bukaci A Gudanar Da Zabe Cikin Kwanciyar Hankali

Tsoffin shugabannin kasar Ghana sun bukaci da a gudanar da zaben shugaban kasa da na 'yan majalisar kasar za a gudanar a kasar cikin kwanciyar hankali sannan kuma bisa inganci ba tare da magudi ba.

Kamfanin dillancin labaran kasar China Xianhua ya jiyo tsoffin shugabannin kasar Ghanan Jerry Rawlings da John Kufour suna bayyana fatan da suke da shi daga hukumar zaben kasar mai cin gashin kanta da kuma sauran jami'an kasar da abin da ya shafa da su yi iyakacin kokarinsu wajen ganin an gudanar da zaben cikin inganci da kuma kwanciyar hankali.

A yayin zaben dai wanda za a gudanar da shi a watan Nuwamba mai zuwa za a zabi shugaban kasa ne da kuma 'yan majalisu 275 na kasar.

Shugaban kasar Ghanan John Dramani Mahama, wanda shi ma dan takara ne a zaben watan Nuwamban yayi alkawarin gudanar da zabe mai inganci ba tare da magudi ba a yayin zaben.