UNICEF Ya Kara Yawan Tallafin Da Zai Baiwa Najeriya
Asusun tallafawa kananan yara na MDD (UNICEF) ya bayyana cewa, ya kara yawan kudaden agajin jin kai da zai samar a Najeriya, daga dala miliyan 55 zuwa dala miliyan 115.
Asusun ya bayyana cewa, an dauki wannan mataki ne don ganin ya kai ga dukkan yankunan da rikicin Boko Haram ya shafa a yankunan arewa maso gabashin Najeriya.
A cewar asusun na Unicef, an kara samun sabbin yankuna da ke jiran irin wadannan kayayyakin agajin musamen ga yara kanana sakamakon hare-haren Boko Haram.
Bayanai daga kasar sun nuna cewa kimanin kananan yara 400,000 'yan kasa da shekaru biyar a jihohi uku na yankin arewa maso gabashin Najeriya, za su fuskanci matsalar karancin abinci mai gina jiki. Akwai kuma sama da mutane miliyan hudu da ke fuskantar karancin abinci da kuma wasu mutane 65,000 da ke fama da yunwa, galibinsu a jihar Borno da rikicin Boko Haram din ya fi yiwa ta'adi.