Kungiyar AU za Ta tura Tawagarta zuwa kasar Burundi
(last modified Tue, 23 Feb 2016 15:26:49 GMT )
Feb 23, 2016 15:26 UTC
  • Kungiyar AU za Ta tura Tawagarta zuwa kasar Burundi

Tawagar Ta kumshi shugabanin kasashen Afirka biyar da za su yi kokari wajen tattaunawa da bangarorin siyasar, domin yayyafawa rikicin siyasar kasar

Kamfanin dillancin Labaran kasar Faransa daga birnin Johannesburg ya nakalto fadar shugaban kasar Afirka ta kudu a yau Talata ta sanar da cewa a ranaikun 25 da 26 ga wannan watan Favrayun da muke ciki ne tawagar kungiyar kasashen Afirkan da ta kumshi shugabani da ministocin kasashen kalkashin jagorancin shugaban kasar Afirka ta kudu Jacob Zuma za ta kasance a birnin Bujunbura fadar milkin kasar Burundi.

Baya ga Shugaban tawagar a kwai shugaban kasar Murtaniya Wul Abdul-Aziz, Maki Sal na kasar Senegal, Ali Bango na kasar Gabon sai kuma Firaministan kasar Habasha Hailemariam Desalegn.

A baya dai kungiyar ta AU ta dauki kudirin aikewa da Dakarun tabbatar da tsaro da Sulhu zuwa kasar ta Burundi, amma ganin cewa gwamnatin ta Bujunbura ta nuna rashin amincewarta, a karshen watan Janairun da ya gabata kungiyar ta dakatar da wannan kuduri.

Sanarwar ta fadar shugaban kasar Pretoria ta ce tawagar za ta gana da manyan jami'an gwamnatin kasar Burundin da kuma shugabanin 'yan adawa domin warware matsalar Siyasa da kasar ke fuskanta.

Tun cikin watan Avrilun shekarar da ta gabata ce kasar ta Burundi ta fada cikin rikicin siyasa, yayin da Shugaban Nkurinziza ya bayyana sha'awarsa na tsayawa takara, rikicin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane da dama.