Sudan Ta Yi Fatali Da Rahoton Amnesty
Gwamnatin Sudan ta yi wasti da rahoton kungiyar Amnesty wanda ke cewa dakarun kasar sunyi amfani da makamai masu guba a yankin Darfur.
Gwamnatin Sudan ta ce ko kadan babu kamshin gaskiya a cikin wannan rahoto.
A wata hira da kanfanin dilancin labaren faransa na AFP kakakin rundinar sojin kasar Ahmed Khalifa al-Shami, ya ce bai ga abunda zai sa har suyi amfani da makami mai guba ba, kasancewa babu ma 'yan tawayen masu yawa a yankin.
hakazalika a cewar mi zai sa ayi amfani da irin wadanan makamai a daidai lokacin gwamnatin kasar ta shiga shirin tattaunawar siyasa domin shawo kan rikicin dake tsakaninta da 'yan tawayen.
a jiya ne dai kungiyar kare hakkin bil adama ta kasa da kasa Amnesty International, ta zargi sojojin gwamnatin Sudan da hallaka fararen hula da dama ta hanyar amfani da makamai masu guba a yankin na Darfur.