Sudan Ta Kudu Ta Amince Da Girke Dakarun Afirka A cikinta.
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i11845-sudan_ta_kudu_ta_amince_da_girke_dakarun_afirka_a_cikinta.
Gwamnatin Kasar Sudan Ta Kudu Ta Yarda Da Shawarar Majalisar Dinkin Duniya Ta Girke Sojojin Nahiyar Afirka A cikinta
(last modified 2018-08-22T06:59:01+00:00 )
Oct 02, 2016 03:09 UTC
  • Sudan Ta Kudu Ta Amince Da Girke Dakarun Afirka A cikinta.

Gwamnatin Kasar Sudan Ta Kudu Ta Yarda Da Shawarar Majalisar Dinkin Duniya Ta Girke Sojojin Nahiyar Afirka A cikinta

Jaridar Sudan Tribune ta buga labarin da ke cewa; Gwamnatin Sudan ta kudu ta sanar a jiya asabar cewa; An kammala tuntubar bangarorin da su ka kamata domin girke dakarun yankin da zummar kawo karshen rikicin da ake yi.

Manufar girke dakarun yankin na Afirka a cikin Kasar ta Sudan ta kudu, shi ne bada kariya ga cibiyoyin gwamnati da  filin saukar jiragen sama na Juba, da kuma dawo da doka da oda.

Bayan rikicin da ya barke a babban birnin  Sudan ta Kudu, Juba, shugabannin kasashen Afirka sun bukaci aikewa da dakarun tabbatar da zaman lafiya na yanki zuwa kasar.