Jingine Tattaunawar Siyasa A Kasar Gunea Conakry
An dakatar da tattaunawar da ake yi a tsakanin gwamnati da kuma 'yan hamayyar kasar Guinea Conakry
Kamfanin Dillancin Labarun Faransa ya ambato cewa; Mahalarta taron da ake yi wa lakabi da : Tattaunawar Siyasa Ta kasa" wacce aka fara a karshen Satumba, sun ce za a jingine ta a ranar 4 ga watan Oktoba.
Jingine tattaunawar dai yana da alaka ne da bullowar sabani a tsakanin wakilan gwamnati da kuma na 'yan hamayya akan yadda za a tsara zaben kananan hukumomi.
Ganawar da aka yi a tsakanin shugaban kasa Alfa Konde da kuma Pira minista wanda kuma shi ne jagoran 'yan hamayya, Cellou Dalein Dilallo ne a ranar 1 ga watan Satumba ne masomin bude tattaunawar.
Masu halartar taron dai sun kunshi wakilan gwamnati da 'yan hamayya da kungiyar fararen hula da kuma wasu kungiyoyin kasa da kasa.
Muhimman batutuwan da tattaunawar ta maida hankali akansu dai sun kunshi, aiwatar da cimma yarjejeniyar da aka cimma a ranar 20 ga watan August 2015 akan zaben shugaban kasar. Haka nan kuma sakin fursunonin siyasa da aka kama bayan rikicin zaben shugaban kasa.