Gwamnati Somaliya Ta Ja-Kunnen Amurka!
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i11854-gwamnati_somaliya_ta_ja_kunnen_amurka!
Kasar Somaliya Ta Gargadi Amurka Akan Hari A cikin Kasar.
(last modified 2018-08-22T06:59:01+00:00 )
Oct 02, 2016 03:13 UTC
  • Gwamnati Somaliya Ta Ja-Kunnen Amurka!

Kasar Somaliya Ta Gargadi Amurka Akan Hari A cikin Kasar.

A jiya asabar ne dai gwamnatin ta kasar Somaliya ta bukaci Amurkan ta yi karin bayani akan harin da ta kai a yankin Galmundug mai cin gashin kai a arewacin Somaliya.

A ranar larabar da ta gabata ne dai gwamnatin Amurkan ta sanar da cewa ta kai wa kungiyar al-shabab hari a yankin na Galmundug tare da kashe hudu daga cikinsu.

Sai dai harin da Amurkan ta kai ya kashe mutanen da ba su da alaka da kungiyar ta al-shabab.

Wasu rahotanni sun tabbatar da cewa, a wani harin da Amurkan ta kai a ranar alhamis din da ta gabata, mutane 20 fararen hula su ka jikkata da kuma mutuwa.

A cikin watannin bayan nan dai, sojojin na Amurka sun kara yawan hare-haren da su ke kai wa a kasar Somaliya da sunan fada da kungiyar al-shabab.