Wasu 'Yan Bindiga Sun Kashe Mutane Akalla 9 A Sudan Ta Kudu
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i11866-wasu_'yan_bindiga_sun_kashe_mutane_akalla_9_a_sudan_ta_kudu
Wasu mutane dauke da makami da har yanzu ba a gane ko su wane ne ba sun kai wani mummunan hari ga wasu matafiya a Kudancin garin Juba babban birnin kasar Sudan ta Kudu inda wasu rahotannin suka ce sun kashe da kuma raunana wasu daga cikinsu.
(last modified 2018-08-22T06:59:01+00:00 )
Oct 02, 2016 07:50 UTC
  • Wasu 'Yan Bindiga Sun Kashe Mutane Akalla 9 A Sudan Ta Kudu

Wasu mutane dauke da makami da har yanzu ba a gane ko su wane ne ba sun kai wani mummunan hari ga wasu matafiya a Kudancin garin Juba babban birnin kasar Sudan ta Kudu inda wasu rahotannin suka ce sun kashe da kuma raunana wasu daga cikinsu.

Kamfanin dillancin labaran Xianhua na kasar China ya jiyo kakakin 'yan sandan Sudan ta Kudun Daneil Justin Bulo yana cewa har ya zuwa yanzu ba a gano mutanen da suka kai harin ba, yana mai cewa maharan sun kai hari ne kan wata mota da take dauke da matafiya.

Kakakin ya kara da cewa ya zuwa yanzu dai an tabbatar da mutuwar mutane 9 da kuma wasu taran da suka sami raunuka wadanda tuni a ka kai su asibiti don yi musu magani.

Kasar Sudan ta Kudun dai ta shiga cikin rikice rikice da yakin basasa tun bayan da shugaban kasar Salva Kiir ya zargi mataimakinsa Riek Machar da kokarin yi masa juyin mulki lamarin da yayi sanadiyyar mutuwar dubban mutane.