Najeriya ta shigar da kara a kan wasu kamfanoni man fetur
Gwamnatin Najeriya ta kai karan wasu kamfanonin Man fetur na kasa da kasa da suke hako da Man fetur ba kan ka'ida ba a cikin kasar
A yayin zaman kotun, wakilan kamfanin Chevron na kasar Amurka da Total na kasar Faransa sun kasa gamsar da kotu a kan karar da ta shigar na ta kawo karshen zarkin da aka yi a kan su na sayar da danyar man na bilyoyin Dalar Amurka ba kan ka'ida. Kamfanonin Man ta Chevron da Total na daga cikin Kamfanoni 15 da Gwamnatin Najeriya ta shigar da su kotu domin a biya ta diya na dala bilyan 15 zuwa 17 sanadiyar danyar da suka fitar ba kan ka'ida ba daga shekarar 2011 zuwa 2014.
Bayan sauraren dalilan bangarorin biyu, babban alkali na kotun daukaka kara daga birnin Legas ya ki amincewa da bukatar wakilan kamfanoni na watsi da karar da Gwamnati ta shigar, sannan ya sanar da ranar 25 ga watan Oktoba da domin ci gaba da sauraren karar.
Tun bayan da Shugaba Buhari ya dare kan karagar milki a watan Mayun shekarar 2015 ya yi alkawarin yaki da cin hanci da rashawa tare kuma da kwato kudaden Gwamnatin da aka babakere da su.
A watan Yunin shekarar da ta gabata,Shugaba Buhari ya bada umarni na hana shigar jiragen ruwa masu dakon danyan Man 113,sanadiyar suna fitar da Man kasar ba tare da sanin Gwamnati ba.