An sanar da kwanaki uku na zaman makoki a kasar Ethiopia
Gwamnatin Ethiopia ta sanar da kwanaki uku na zaman makoki a fadin kasar
Gwamnatin ta Habasha ta sanar da wannan zaman makoki na kwanaki uku bayan aukuwar wani turmutsitsi da ya yi sanadiyar mutuwar Mutane kimanin 52, wannan turmutsitsi ya gudana ne a garin Bishoftu, yayin bukukuwan gargajiya da ‘yan kabilar Oroma suka yi jiya lahadi, shi dai wannan biki ana gudanar da shi a karshen wata shekara domin murnar girbe amfanin gonar bana
A gefen wannan biki wani gungu daga cikin 'yan adawar Gwamnati sun gudunar da zanga-zanga domin nuna rashin jin dadin su kan matakan da Gwamnati ke dauka na wargaza 'yan adawa musamman ma kan yadda jami'an tsaro ke amfani da karfi wajen tarwatsa su a duk lokacin da suke gudanar da zanga-zanga.
Domin tsoratar da su,jami'an 'yan sanda sun yi amfani da harshashin roba, lamarin da ya tsoratar da Al'umma gudu,inda suka dinga take juna domin tsira da rayuwar su.
A bangaren 'yan adawa sun ce wadanda suka mutu sun fi mutane dari daya.