Ziyara Mahamadu Isufu A Najeriya
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i11932-ziyara_mahamadu_isufu_a_najeriya
Shugaba Mahamadu Isufu na Jamhuriya Nijar na wata ziyara aiki da sada zumunta ta kwanaki biyu a Najeriya.
(last modified 2018-08-22T06:59:01+00:00 )
Oct 04, 2016 02:26 UTC
  • Ziyara Mahamadu Isufu A Najeriya

Shugaba Mahamadu Isufu na Jamhuriya Nijar na wata ziyara aiki da sada zumunta ta kwanaki biyu a Najeriya.

Wata sanarwa ta fadar shugaban Nijar, ta ce da yammacin Ranar Lahadi ne shugaba Mahamadu Isufu ya bar Yamai inda ya nufi Abuja babban birnin Tarayya Najeriya.

Nijar da Najeriya na tafiyar da huldar dangantaka da abokantaka a karkashin kwamitin hadin gwiwar dangantaka ta tsawon shekaru fiye da arba'in.

Baya ga batun yaki da kungiyar Boko Haram, shugabannin biyu zasu tattauna batutuwan tattalin arziki, har ma da wasu batutuwan dake shafar nahiyar Afrika da ma duniya a halin yanzu, a yayin wannan ziyara.

Musammun ma game da batun yaki da 'yan ta'addan Boko Haram, rundunar sojojin Nijar da Najeriya, na cikin rundunar hadin gwiwa tare da sauran rundunonin kasashen Chadi, Kamaru domin murkushe kungiyar Boko Haram.

Alkaluma dai sun nuna cewa dalilin matsalar Boko Haram, kusan mutane dubu 20 aka kashe kana fiye da wasu miliyan 2.6 suka kaura daga muhallinsu tun daga shekarar 2009.

A Nijar, yankin jihar Diffa dake kudu maso gabashi, mai iyaka da Najeriya, ya kasance wani fagen daga tun yau da shekaru biyu, kuma munanan hare haren kungiyar Boko Haram tun daga sansanoninta dake Najeriya, sun yi sanadiyyar mutuwar daruruwan fararen hula da sojoji da janyo miliyoyin 'yan gudun hijira a Nijar da  Najeriya. 

Kasashen Najeriya da Nijar dai na matukar bukatar juna, musamman a daidai wannan lokaci da ake bukatar ganin bayan kungiyar Boko Haram dake zamen babbar barazana a yankin.

Kasashen biyu na samun taimakon soji daga kasashen Kamaru da Chadi kasancewar a cikin rundinan hadin gwiwar kasashen yankin dake yaki da Boko haram.

A baya bayan nan dai hadin gwiwar kasahen Chadi sun hallaka 'yan ta'addan Boko Haram 123, a ci gaba da samamen da suke kaiwa a yankin Diffa dake kudu maso gabashin kasar.

Hakazalika, farmakin na hadin gwiwa da Chadi na tafiya a lokaci guda da wani hadin gwiwa na dakarun Nijar da Najeriya wanda shima ya yi nasara kwace mahimman yankuna daga hannun 'yan ta'addan na boko Haram a Najeriya da suka hada da Damasack, Abadan da Gachagar.

Nijar dai na raba iyaka da Najeriya mai fadin kilomita 1,500 kuma ko baya ga hakan kasashen biyu na amfani da harsuna iri daya da suka hada da Hausa, Kanuri da kuma Fulatanci.