Jami'ar Azhar Ta Sake Jaddada Wajibcin Fada Da Ta'addanci
Shugaban jami'ar Al-Azhar ta kasar Masar Sheikh Ahmad al-Tayyib ya sake jaddada wajibcin fada da ta'addanci yana mai cewa ayyukan ta'ddanci sun yi hannun riga da koyarwar addinin Musulunci da sauran saukakkun addinai.
Rahotanni sun bayyana cewar Sheikh Ahmad al-Tayyib ya bayyana hakan ne a jawabin da ya gabatar a wani taro da aka gudanar a yau din nan inda ya ce ko shakka babu 'yan ta'adda sun ha'inci addinin Musulunci da ma sauran saukakkun addinai don kuwa dukkanin wadannan addinai babu ruwansu da ayyukan ta'addanci.
Shugaban jami'ar ta Al-Azhar ya kara da cewa addini da ayyukan ta'addanci wasu abubuwa ne guda biyu da suka yi hannun riga da junansu, don haka yace babban kuskure ne kokarin da wasu suke yi na jingina ayyukan ta'addanci ga addinin Musulunci.
Daga karshe dai Sheikh Ahmad Al-Tayyib ya sake jaddada aniyar jami'ar Al-Azhar din na ba da hadin kai ga hukumomi a fadar da ake yi da ta'addanci.