Gwamnatin Kasar Demokradiyar Congo Ta Soki Ministan Harkokin Wajen Kasar Faransa
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i11971-gwamnatin_kasar_demokradiyar_congo_ta_soki_ministan_harkokin_wajen_kasar_faransa
Sukar Kasar Jamhuriyar Congo Ga Faransa
(last modified 2018-11-18T05:33:40+00:00 )
Oct 04, 2016 15:25 UTC
  • Gwamnatin Kasar Demokradiyar Congo Ta Soki Ministan Harkokin Wajen Kasar Faransa

Sukar Kasar Jamhuriyar Congo Ga Faransa

Gwmanatin Kasar Demokradiyyar Congo ta soki ministan harkokin wajen kasar faransa, saboda tsoma baki a harkokin cikin gidanta.

Kakakin gwamnatin kasar Jamhuriyar Demokradiyyar Congo, Lambert Mende ya yi watsi da maganar da ministan harkokin wajen Faransa Jean-Marc Ayrault ya yi na wajabcin yin aiki da kundin tsarin mulkin kasar ta Demokradiyyar Congo.

A jiya litinin ne dai ministan harkokin wajen kasar Faransa Jean Marc Ayrault ya kira yi shugaba  Joseph Kabila da ya girmama kundin tsarin mulkin kasar, ya ki yin takarar shugaban kasar a karo na gaba.

Yan hamayyar kasar suna gudanar da Zanga-zangar yin kira ga shugaban kasar Joseph Kabila da ya yi murabus, kada ya sake tsayawa takara.

Za a gudanar da zaben shugaban kasar ne dai a watan Decemba a 2018.