'Yan Hamayyar Siyasar Zambia Za Su ci gaba Da Yin Zanga-zanga.
Za a ci gaba da zanga-zangar kin jinin gwamnati a Zambia
"Yan hamayyar siyasa a kasar Zambia, sun yi watsi da dokar hana yin Zanga-zangar nuna kin jinin gwamnati.
Kakakin jam'iyyar "Gamayya Domin Ci Gaban Kasa' Charles Kakoma ya bayyana cewa; 'Yan siyasar kasar basu yarda da cewa; al'ummar ce su ka zabi Edgar Lungu ba, saboda haka za su ci gaba da yin zanga-zangar nuna kin amincewa da gwamnatinsa.
Charles Kakoma ya kara da cewa; Jam'iyyun hamayyar kasar basu yarda da cewa zaben da aka yi na shugaban kasa, ya kasance a karkashin dokokin zaben kasar ba ne, saboda haka ba a yi shi kan ka'ida ba.
A farkon wannan makon, 'yan majalisa 58 da su ka fito daga jam'iyyun hamayya, sun fice daga zauren da shugaban kasar Lungu ya ke yin jawabi.
An yi zaben shugaban kasar ta Zambia ne a ranar 11 ga watan August na wannan shekarar. Jam'iyyun hamayyar sun nuna kin amincewarsu da sakamakon zaben.