Kungiyar Tarayyar Afrika Ta Jaddada Wajabcin Samun Zaman Lafiya A Kasar Habasha
Shugabar Kungiyar Tarayyar Afrika ta jaddada wajabcin daukan matakan wanzar da zaman lafiya da sulhu a kasar habasha.
A bayanin da shugabar kungiyar tarayyar Afrika Nkosazana Dlamini-Zuma ta fitar a jiya Talata yana dauke da cewa: Kungiyar Tarayyar Afrika tana jaddada yin kira ga gwamnatin kasar Habasha kan hanzarta gudanar da bincike dangane da musabbabin faruwar turmitsitsin da aka yi a garin Bishoftu da ke lardin Oromia da ya kai ga hasarar rayukan mutane fiye da 50.
Har ila yau Nkosazana Dlamini-Zuma ta bayyana alhini da ta'aziyarta ga iyalan mutanen da suka rasa rayukansu; tana mai jaddada goyon baya kan matakin da mahukuntan Habasha suka dauka na ware kwanaki uku a matsayin hutu a duk fadin kasar domin juyayin hasarar rayukan da aka yi a tirmitsitsin garin na Bishoftu.
A ranar Lahadin da ta gabata ne 'yan sandan Habasha suka harba iskar gas mai sanya hawaye tare da harba bindiga sama da nufin tarwatsa wasu gungun jama'a da suke zanga-zangar nuna kin jinin gwamnatin kasar a lokacin bikin al'ada ta karshen lokacin damina a garin Bishoftu da ke lardin Oromia a gabashin birnin Addis Ababa fadar mulkin kasar lamarin da ya haifar da tirmitsitsin jama'a da ya kai ga hasarar rayukan mutane akalla 52 tare da jikkatan wasu da dama.