Al'ummar Habasha Sun Gudanar Da Zanga-Zangar Nuna Kin Jinin Gwamnatin Kasar
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i12025-al'ummar_habasha_sun_gudanar_da_zanga_zangar_nuna_kin_jinin_gwamnatin_kasar
Al'umma a yankuna daban daban a lardin Oromia na kasar Habasha sun gudanar da zanga-zangar nuna kin jin gwamnatin kasar.
(last modified 2018-08-22T06:59:02+00:00 )
Oct 05, 2016 13:00 UTC
  • Al'ummar Habasha Sun Gudanar Da Zanga-Zangar Nuna Kin Jinin Gwamnatin Kasar

Al'umma a yankuna daban daban a lardin Oromia na kasar Habasha sun gudanar da zanga-zangar nuna kin jin gwamnatin kasar.

Kamfanin dillancin labaran Fransa ya habarta cewa: Al'ummar a yankunan daban daban na kasar Habasha musamman a lardunan Oromia da Amhara sun gudanar da zanga-zangar nuna kin jinin gwamnatin kasar. Zanga-zangar da ta samu halattar 'yan adawar siyasa sun jaddada bukatar sakin 'yan adawa da ake tsare da su a gidajen kurkuku.

Kasar Habasha ta kara shiga cikin dambaruwar siyasa ce tun bayan tirmitsitsin da ya faru a garin Bishoftu a ranar Lahadin da ta gabata da ya lashe rayukan mutane akalla 52 tare da jikkatan wasu da dama sakamakon harba iskar gas mai sanya hawaye da bindiga a sama da 'yan sanda suka yi da nufin tarwatsa masu zanga-zangar nuna adawa da gwamnatin kasar.