Sudan Ta Kudu : Dakarun MDD Basu Kare Fararen Hula Ba
Kungiyar (CIVIC) dake fafatukar ganin an kare fararen hula a lokacin rikice-rikice, ta soki lamarin dakarun MDD a Sudan ta Kudu wanda ta ce basu kare fararen hula ba a lokacin da rikici ya barke tsakanin sojoji da 'yan tawaye a birnin Juba.
A rahoton data fitar Jiya Laraba kungioyar ta ce dakarun na MDD basuyi aikin daya rataya akansu ba na kare fararen hula.
kungiyar ta ce wasu daga cikin dakaraun sun bar wurin aikinsu, kana a inda ya kamata a ce sun je don kare fararen hula ba'a gansu ba.
A hannu daya kuma kungiyar ta ce, a lokacinda aka kaiwa wasu jami'an agaji na ketare hari dakarun na MDD basu kai dauki ba.
Kungiyar ta kuma bukaci MDD data dauki mataki akan wannan batu don hukunta duk jami'anta dake da laifi.
An dai shafe wata biyu ana bincike kan zargin dakaraun na MDD da rashin tabaka komai wajen kare fararen hula a lokacin rikicin daya faru tsakanin sojojin gwamnatin Salva Kiir da kuma wadanda ke biyaya ga tsohon mataimakinsa kana jagoran 'yan tawaye Riak Mashar a cikin watan Yuli daya gabata.