Sojojin Nigeria Sun Hana Wani Dan Kunan Bakin Wake Shiga Tsakaninsu
Sojojin Nigeria a birnin Maiduguri na jihar Borno sun sami nasarar hana wani dan kunan bakin waki shiga tsakaninsu a safiyar yau Alhamis.
Jaridar Daily Trust ta Nigeria ta nakalto kakakin sojojin Nigeria Conar Sani Usman ya bayyana a safiyar yau cewa dakarun Operation Lafiya Dole sun sami nasarar gano wani dan kunan bakin wake wanda ya yi damara da boma bomai shiga tsakaninsu, sun kuma kwace bom din ba tare da wata matsala ba.
Usman ya kara da cewa mutumin ya fito daga wani kauye mai suna Ali-dawari kilomita 4 daga inda sansanin sojojin yake a Jidari Polo, sannan ya ki tsayawa bayan wani gargadi da suka yi masa. daga nan ne jami'ansu kwararru a harkar boma boma suka tunkareshi suka kuma sami nasara lalata boma boman da ya yi riga da su.
Labrin bai bayya makomar dan kunan bakin waken ba. Mayakon Boko haram dai sun takaita ga kai hare haren kunan bakin wake kan mutanen gari da kuma jami'an tsaron Nigeria bayan an karbe yankunan da suke iko da su, an kuma karya logunsu a mafi yawan hare hare da suke kaiwa.