Gwamnatin Jihar Kaduna Ta Haramta Ayyukan Kungiyar Harkar Musulunci A Jihar
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i12112-gwamnatin_jihar_kaduna_ta_haramta_ayyukan_kungiyar_harkar_musulunci_a_jihar
Rahotanni daga Nijeriya sun bayyana cewar gwamnatin Jihar Kaduna da ke arewacin kasar ta haramta dukkanin ayyukan kungiyar harkar Musulunci a Nijeriya karkashin jagorancin Sheikh Ibrahim El-Zakzaky.
(last modified 2019-01-16T04:00:45+00:00 )
Oct 07, 2016 14:54 UTC
  • Gwamnatin Jihar Kaduna Ta Haramta Ayyukan Kungiyar Harkar Musulunci A Jihar

Rahotanni daga Nijeriya sun bayyana cewar gwamnatin Jihar Kaduna da ke arewacin kasar ta haramta dukkanin ayyukan kungiyar harkar Musulunci a Nijeriya karkashin jagorancin Sheikh Ibrahim El-Zakzaky.

A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan jihar Kadunan Malam Nasiru El-Rufai wato Samuel Aruwan ya sanya wa hannu ya ce gwamnatin ta haramta ayyukan kungiyar ta harkar Musuluncin a jihar bisa saboda karfin da tsarin mulki ya ba ta na tabbatar da tsaro da bin doka da oda a jihar.

Sanarwar ta kara da cewa dokar haramcin wacce za ta fara aiki a yau din nan Juma'a ta tanadi daurin na shekaru bakwai ko kuma cin tara ko kuma duka biyun kan duk wanda aka samu ya karya wannan dokar da kuma gudanar da ayyukansa da sunan kungiyar.

Fitar da wannan dokar dai ta biyo bayan rikicin da ya faru ne a shekarar da ta gabata tsakanin sojojin Nijeriya da 'yan kungiyar ta IMN a garin Zariya inda sojojin Nijeriyan suka kashe daruruwan 'yan kungiyar saboda zargin cewa sun tsare wa babban hafsan hafsoshin sojojin Nijeriyan Janar Yusuf Tukur Brutai.