Adadin Wadanda Aka Kashe A Habasha Sun Karu
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i12139-adadin_wadanda_aka_kashe_a_habasha_sun_karu
Karuwar Zanga-zangar Kin Jinin Gwamnati A Kasar Habasha
(last modified 2018-08-22T06:59:03+00:00 )
Oct 08, 2016 03:26 UTC
  • Adadin Wadanda Aka Kashe A Habasha Sun Karu

Karuwar Zanga-zangar Kin Jinin Gwamnati A Kasar Habasha

An kara samuwar wadanda su ka rasa rayukansu a kasar Habasha, bayan Zanga-zangar da aka yi a garin Bishopto da ke kudancin kasar.

Majiyar gwamnati ta ce adadin wadanda su ka rasa rayukansu a rikicin da kasar ta ke fuskanta sun kai 55, sai dai majiyar 'yan hamayya ta ce adadin sun dara haka da dama.

Masu zanga-zangar dai suna nuna kin amincewarsu ne da rashin adalcin da su ke fuskanta daga gwamnatin kasar a tsawon shekara da shekaru.

A cikin watannin bayan nan dai zanga-zanga kin jinin gwamnati ta tsananta a cikin kasar ta Habasha.