An Kashe Mutane Shida A Kasar Somaliya
Oct 08, 2016 03:28 UTC
Riciki A yankin Putland ya yi sanadin mutuwar mutane 6.
Kamfanin Dillancin Labarun Faransa ya ambaci cewa; Rikici a tsakanin yankunan Putland da Galmudug na Somaliya ya yi sanadin mutuwar mutane shida.
Bangarorin biyu dai sun fada cikin rikici ne, bayan harin da Amurka ta kai wa yankin a cikin watan Satumba, wanda ya yi sanadin mutuwar mutane 13. Yankin Galmudug ya zargi yankin Putland da bai wa Amurka bayanai na kuskure da ta dogara da su wajen kai harin.
Jami'an tsaron yankunan biyu sun yi taho mu gama na tsawon sa'oi a jiya juma'a a yankin Galkayo.
Somaliya dai tana fama da matsalar rashin tsaro tun a 1991.
Tags