Jami'an Tsaron Burkina Faso Sun Kashe Wasu 'Yan Bindiga A Gabashin Kasar
(last modified Sun, 09 Oct 2016 06:18:33 GMT )
Oct 09, 2016 06:18 UTC
  • Jami'an Tsaron Burkina Faso Sun Kashe Wasu 'Yan Bindiga A Gabashin Kasar

Majiyar tsaron Burkina Faso ta sanar da cewa: Jami'an tsaron kasar sun kashe wasu 'yan bindiga biyu da ake zargin 'yan ta'adda ne a yankin gabashin kasar.

Majiyar tsaron Burkina Faso ta sanar da cewa; Wasu gungun 'yan bindiga hudu sun kai farmaki kan jami'an tsaron Burkina Faso a yankin gabashin kasar da nufin kwace makamai lamarin da ya haifar da dauki ba dadi a tsakanin bangarorin biyu da ya kai ga halakar 'yan bindiga biyu tare da jikkata guda, 

Majiyar ta kara da cewa babu wata alama da take fayyace gungun 'yan bindiga mambobin wata kungiyar ta'addanci ne amma za a ci gaba da gudanar da bincike domin gano hakikaninsu.