'Yan Uwa Musulmi Sun gudanar da zangar zangar Lumana a Najeriya
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i12226-'yan_uwa_musulmi_sun_gudanar_da_zangar_zangar_lumana_a_najeriya
Dariruwan 'yan uwan musulmi mabiya mazhabar Shi'a, almajiran shekh Elzakzaky sun gudanar da zanga-zangar Lumana domin nuna adawa da matakin da Gwamnatin Jihar Kaduna ta dauka na hanasu gudanar da aikace-aikacen su.
(last modified 2018-08-22T06:59:03+00:00 )
Oct 09, 2016 14:18 UTC
  • 'Yan Uwa Musulmi Sun gudanar da zangar zangar Lumana a Najeriya

Dariruwan 'yan uwan musulmi mabiya mazhabar Shi'a, almajiran shekh Elzakzaky sun gudanar da zanga-zangar Lumana domin nuna adawa da matakin da Gwamnatin Jihar Kaduna ta dauka na hanasu gudanar da aikace-aikacen su.

Kamfanin dillancin Labaran Irna na kasar Iran ya habarta cewa a yau Lahadi, Dariruwan Al'ummar musulmi mabiyar mazhabar shi'a almajiran shekh Ibrahim Elzakzaky sun gudanar da zanga-zangar Lumana domin nuna adawar su da wani sabon gudiri da Gwamnatin jihar Kaduna ta dauka na haramta aikace-aikace su tare da neman Gwamnatin kasar ta gaggauta sakin jagoran su shekh Ibrahim Elzakzaky a gariruwan Kaduna da Zariya.

Mahalarta zanga-zangar dake dauke da kyallaye rubuce da neman janye kudirin da Gwamnatin Jihar kaduna ta dauka tare da neman a gaggauta sakin Jagoran su shekh Ibrahim Elzakzaky sun yi tattaki har zuwa gidan Gwamnatin jihar domin bayyana adawar su da wannan doka.

A bangare guda mai magana da yawun 'yan uwan musulmin na Jihar Kaduna ya bayyana cewa ba za su yi da'a ga wannan doka ba kuma za su ci gaba da gudanar da addininsu kamar yadda suka saba sannan za su kalubalanci Gwamnati Jihar da Gwamnatin Tarayyar kan irin babbancin da ake kwada musu a cikin kasar.

A ranar Juma'ar da ta gabata ce Gwamnatin Jihar Kaduna ta sanar da haramta dukkan aikace-aikacen mabiya mazabar Shi'a Almajiran Shekh Ibrahim Yakubu El-zakzaky tare da yin barazanar dauri har na tsahon shekaru bakwai a gidan yari.