Habasha : An Kafa Dokar Ta Baci Na Tsawan Watanni 6
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i12241-habasha_an_kafa_dokar_ta_baci_na_tsawan_watanni_6
Hukumomi a kasar Habasha sun sanar da kafa wata dokar ta baci ta tsawan watannin shida a duk fadin kasar.
(last modified 2018-08-22T06:59:03+00:00 )
Oct 10, 2016 02:23 UTC
  • Habasha : An Kafa Dokar Ta Baci Na Tsawan Watanni 6

Hukumomi a kasar Habasha sun sanar da kafa wata dokar ta baci ta tsawan watannin shida a duk fadin kasar.

Wannan matakin a cewar firaministan kasar Hailemariam Dessalegn, an dau shi ne domin tinkarar tashe-tashen hankalin da suka barke sakamakon zanga-zangar da mazauna yankin Oromia suka yi.

Mista Dessalegn ya kara da cewa, a ranar Asabar data gabata ce majalisar ministocin kasar ta kira taron gaggawa game da halin da kasar ta shiga inda ta tsaida kudurin sabo da tabbatar da zaman lafiya a kasar da tsaron jama'a.

A kwanan baya ne, al'ummar yankin Oromia suka shirya zanga-zangar nuna adawa da gwamnati da neman 'yancin filaye da yadda gwamnati take rushe musu gidaje, lamarin daya kai ga yin arangama da sojoji da 'yan sanda, wanda ya janyo hasara rayuka da jikkatar mutane da dama, kuma yanayin ya ci gaba da tsananta.