Habasha Ta Zargi Masar Da Hannu A Rikicin Kasar
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i12265-habasha_ta_zargi_masar_da_hannu_a_rikicin_kasar
Gwamnatin Kasar Habasha Ta Zargi Masar Da Ingiza Masu Zanga-zangar A Kasar.
(last modified 2018-08-22T06:59:04+00:00 )
Oct 10, 2016 15:27 UTC
  • Habasha Ta Zargi Masar Da Hannu A Rikicin Kasar

Gwamnatin Kasar Habasha Ta Zargi Masar Da Ingiza Masu Zanga-zangar A Kasar.

Ministan Sadarwa kuma kakakin gwamnatin kasar Habasha, Getachew Reda ya ce; Kasashen waje da suka hada da Masar ne su ke ingiza masu zanga-zanga a yankin Oromo.

Ministan na Habasha ya ce; Masar ce ta bada kudade da horo na soja ga yan kungiyar neman 'yancin Oromo da su ke son ballewa daga kasar Habasha.

Bugu da kari, Ministan watsa labarun kuma kakakin gwamnatin Habasha, ya ce; Gwamnatin Masar tana bada dukkanin cikakken goyon baya ga 'yan tawayen kasar.

A cikin watannin bayan nan dai al'ummar Oromo da su ke kaso 60% na al'ummar kasar  sun rika yin zanga-zanga saboda rashin yi musu adalci da gwamnatin kasar ta ke yi.