Somaliya: Asarar Rai Asanadin Tarwatsewar Mota Mai Makare Da Bom
Oct 10, 2016 15:31 UTC
Mutum Guda Ya Mutu A Somaliya Saboda harin ta'addanci
Jami'ian Tsaron Kasar Somaliya Sun sanar da fashewar wata mota mai makare da bama-bamai a birnin Mogadishu wanda ya yi sanadin mutuwar mutum guda.
Bugu da kari, wasu mutane 3 sun jikkata sanadiyyar tashin bom din.
Kamfanin Dillancin Labarun Xinhua ya ambato jami'an tsaron kasar suna cewa; tuni sun kame wani mutum guda wanda su ke zargi da hannu a shirya kai harin.
Kawo ya zuwa yanzu dai babu wanda ya dauki nauyin kai harin, sai dai jami'an tsaron kasar na zargin kungiyar al-shabab.
Tags