Demokradiyyar Congo: Kira Domin Tsananta Taro Akan Iyaka Da Kasar Uganda
Kungiyoyin Fararen Hula Suna Son A tsananta tsaro A Kan Iyaka da Uganda
Kungiyoyin Fararen hula a kasar Demokradiyyar Congo, sun yi kira ga gwamnati da ta tasaurara tsaro akan iyaka da kasar uganda.
Jaridar Lo figaro ta Faransa ta ambato jami'in kungiyar fararen hula ta Kizibo Bin Hangi, a yankin Beni, da ke kundumar Kivo ta Arewa, yana cewa; Da akwai bukatar a tsaurara tsaro akan iyaka da Uganda bayan gwamnati Kampala ta yi zargin cewa ta'adda sun shiga kasarta daga Congon.
Bin Hangi ya kara da cewa; Zargin na kasar Uganda zai iya zama wani dalili da za ta fake da shi domin kai wa kasar Demokradiyyar congo hari.
A yayin taron kasashen yankin ne wanda aka yi a watan Satumba, gwamnatin Uganda zargi gwamnatin Demokradiyya da zaunar da 'yan ta'adda a cikin kasarta.
Tuni dai kasashen yankin su ka bude nazari akan tuhumar ta kasar Uganda.