'Yan tawayen Kasar Sudan Ta Kudu Sun Kashe Mutane Da Dama
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i12274-'yan_tawayen_kasar_sudan_ta_kudu_sun_kashe_mutane_da_dama
Mutane Da Dama Sun Mutu Saboda Harin 'Yan ta'adda.
(last modified 2018-08-22T06:59:04+00:00 )
Oct 10, 2016 15:38 UTC
  • 'Yan tawayen Kasar Sudan Ta Kudu Sun Kashe Mutane Da Dama

Mutane Da Dama Sun Mutu Saboda Harin 'Yan ta'adda.

Kamfanin Dillancin Labarun Reuters ya ambato majiyar ofishin majalisar dinkin duniya a kasar Sudan Ta Kudu, yana cewa; A yau litinin 'yan tawayen da su ke karkashin Reikh Machar sun kai harin da ya kashe fararen 21 da kuma jikkata wasu 20.

Ofishin majalisar dinkin duniyar da ke kasar ta Sudan ta kudu, ya yi kira ga 'yan tawayen da su dakatar da kai harin.

Harin na yau ya zo ne a daidai lokacin da gwamnatin kasar a karkashin Shugaban Silva Kir ta aike da tawagar kwararru na soja da siyasa zuwa yankin Rodyi da sauran yankunan da su ke kan iyaka da Uganda da Demokradiyyar Congo, domin nazarin kai da komowar 'yan tawaye.

A cikin makwannin bayan nan ne dai madugun 'yan tawayen Reikh Machar da ya fice daga kasar, ya shelanta yaki akan gwamnatin kasar.