An Hana Yan gudun Hijira Daga Nigeria Ficewa Daga Kasar Zuwa Libya
Hukumar shige da fice a tarayyar Nigeria ta bayyana cewa ta gano wasu yan kasar
Hukumar shige da fice a tarayyar Nigeria ta bayyana cewa ta gano wasu yan kasar wadanda suke da anniyar ficewa daga kasar zuwa kasar Libya kuma ta hanasu fita.
Shafin yanar gizo na Afrika times ya nakalti Alhaji Alfa Ahmed shugaban hukumar shige da fice na jihar katsahina yana bayyana haka a jiya talata. Ahmad ya kara da cewa sun gano mutanen ne a kusa da dan iyakar nigeria da Niger, inda da farko suna sun kaiwa garin agades na jumhuriyar Niger daga can kuma su wace kasar Libya sannan zuwa turai.
Alhaji Alfa ya dukkan mutanen da aka kaman basu da takardun shaida na tafiye tafiye tare da su. Don haka suna nufin yin tafiyar ne ta barauniyar hanya.