Kudirin kasashen Afikra na yaki da rashin tsaron ruwa
Kasashen Afirka na gudanar za su fara gudanar taro kan harakokin tsaron ruwa a birnin Lome fadar milkin kasasr Togo.
A yayin shirye-shriyan taron, Ministan harakokin wajen kasar Togo Profesa Robert Dussey ya tabbatar da mahimancin wannan taro sannan ya bayyana shirin kasar sa na aiki tare da kasashen Afirka wajen yaki da rashin tsaro a ruwan kasashen.
Mista Dussey ya bayyana mahimancin yaki da bariyin ruwa tare kuma da kokari wajen tabbatar da tsaro a ruwan yankin Asiya, inda ya kara da cewa kashi 92% na kayayyakin dake shigowa yankin Afikra ta hanyar ruwan Asiya ne, kuma daga cikin kasashen 54 na Afirka, kasashe 33 suna a kan iyakokin ruwa da yankin ne.
A Ranar 15 ga watan Oktaba ne za a buda taron wanda zai samu halartar manyan jami'an kasashen Tarayar Afirka.