Ficewar Madugun 'yan tawayen Sudan ta kudu daga kasar Sudan
Shugaban 'yan tawayen sudan ta kudu dake samu mafaka a kasar Sudan tun bayan rikicin baya-bayan nan na birnin Juba ya bar birnin Khartum zuwa kasar Afirka ta kudu.
A yayin tashin sa daga filin jirgin saman Khartun, Riek Machar ya bayyana cewa zai je kasar Afirka ta kudun ne domin neman magani, to saidai bayan kasar Afirka ta kudu Madugun 'yan tawayen sudan ta kudun bai bayyana inda zai nufa ba bayan ya samu sauki ba.
Tun a watan Yunin da ya gabata ne, madugun 'yan tawayen sudan ta kudun Riek Machar ya fice daga cikin kasar sa zuwa kasar Sudan bisa da'awar neman magani, wannan kuwa na zuwa ne bayan wani mumunan rikici da ya auku tsakanin sojojin dake biyayya da shi da kuma masu biyayya da Gwamnatin salva keir, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane sama da 300 da yin hijra na wasu dubai daga birnin na Juba.