Tashin Bam a garin Maiduguri na jihar Borno
Rahotanni dake fitowa daga birnin Maiduguri na jihar Borno dake shiyar arewa maso gabashin Najeriya na cewa mutane da dama sun rasa rayukansu sanadiyar tashin wasu bama bamai a safiyar wannan Laraba.
Wadanda suka shaida lamarin sun shaidawa manema labarai cewa bam din ya tashi ne a tashar Muna da safiyar wannan laraba, kuma a gaban idanun su an fitar da gawawwakin Mutane akalla takwas
Saidai har yanzu babu cikakken bayani da ya fito daga jami'an tsaro dangane da Mutanan da suka rasa rayukansu ko kuma suka jikkata sanadiyar tashin wannan bama-bamai.
Birnin na Maiduguri da ya sha fama da hare-haren 'yan kungiyar Boko Haram a baya,an dade ba a samu rahotannin tashin bama-bamai a birnin ba.
Tuni dai kungiyar Boko Haram ta sanar da cewa ita ce ta kai wannan hari.