Majalisar Dokokin Burundi Ta Zabi Ficewar Kasar Daga Kotun ICC
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i12364-majalisar_dokokin_burundi_ta_zabi_ficewar_kasar_daga_kotun_icc
'Yan majalisar dokokin Burundi sunyin na'am da gagarimun rinjaye da kudirin doka na neman ficewar kasar daga kotun hukunta mayan laifuka ta duniya wato ICC.
(last modified 2019-04-27T09:55:10+00:00 )
Oct 12, 2016 12:43 UTC
  • Majalisar Dokokin Burundi Ta Zabi Ficewar Kasar Daga Kotun ICC

'Yan majalisar dokokin Burundi sunyin na'am da gagarimun rinjaye da kudirin doka na neman ficewar kasar daga kotun hukunta mayan laifuka ta duniya wato ICC.

Daga cikin 'yan majalisu 110 da suka halarci zamen, 94 ne suka amunce da kudirin, sai 14 suka wadanda sukayi rawar kuri'arsu da kuma biyu wadanda basu amunce da kudirin ba.

Ye zuwa yanzu dai za'a mika kudirin ga majalisar datijan kasar inda jam'iyya mai mulki a kasar (CNDD-FDD), keda gagarimun rinjaye, kafin daga bisani a mika shi ga shugaban kasar domin rattabama dokar hannu.

kafin hakan dai ministan shari'a na kasar, Aimée-Laurentine Kanyana, ya yi kira ga 'yan majalisun kasar dasu amunce da kudirin don saboda a cewarsa akwai wadanda ke amfani da kotun domin yiwa dokokin kasar karan tsaye.

Wannan matakin na ficewar Burundi daga kotun ta ICC ko kuma CPI shi ne irinsa na farko a tarihi, saidai fa zai iya bude wani sabon babi na maida kasar saniyar ware a idon duniya.