Najeriya / Ashura : Mutane Akallah 10 Sukayi Shahada
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i12373-najeriya_ashura_mutane_akallah_10_sukayi_shahada
Rahotanni daga Najeriya na cewa akallah mutane 10 ne suka rasa rayukansu, kana wasu sama da 50 suka raunana a yayin da jami'an tsaro suka farmawa mabiya mazahabar shi'a dake gudanar da tarurukansu na juyayin Ashura.
(last modified 2018-08-22T06:59:04+00:00 )
Oct 12, 2016 14:17 UTC
  • Najeriya / Ashura : Mutane Akallah 10 Sukayi Shahada

Rahotanni daga Najeriya na cewa akallah mutane 10 ne suka rasa rayukansu, kana wasu sama da 50 suka raunana a yayin da jami'an tsaro suka farmawa mabiya mazahabar shi'a dake gudanar da tarurukansu na juyayin Ashura.

Lamarin dai ya faru ne a garin Funtuwa a lokacin da 'yan sanda da sojoji suka bude wuta kan 'yan Shi'a dake yin tattakin da suka saba yi duk shekara domin tunawa da ranar Ashura kamar yadda kakakin kungiyar reshen Katsina, Husseini Yero ya shaidawa kanfanin dilancin labaren AFP.

Ko baya ga hakan a cewarsa rikicin ya bazu a yankuna da dama dake arewacin kasar.

Abin tuni dai gwamnatocin Katsina, Kebbi da kuma Kano sun haramtawa 'yan Shi'an gudanar da tarurukan na Ashura a wannan shekara.

Wasu bayanai daga jihar kaduna inda gwamnatin yankin ta haramta ayyukan kungiyar 'yan uwa musulmi ko (IMN) an rawaito cewa mutane akalla biyu sun rasa rayukansu a yayin tarurukan na yau.