Ayyukan Hadin Gwiwa Tsakanin Rundunonin Sojin Kasashen Masar Da Rasha
Rundunononin soji na kasar Masar da Rasha na shirin gudanar da wani gagarumin atisayi a karon farko, da nufin karfafa ayyukan hadin gwiwa a tsakaninsu.
Kamfanin dillancin labaran Reaters ya nakalto daga kakain rundunar sojin kasar Masar Muhammad samir cewa, sojojin Masar za su gudanar da atisayi a karon farko tare da takwarorinsu na Rasha, wanda za a fara daga ranar 15 ga wannan wata na oktoba 26.
A cikin wannan makon ne dai kasar Masar ta kada kuri'ar amincewa da daftarin kudirin da kasar Rasha ta gabatar a gaban kwamitin tsaron majalisar dinkin duniya, da ke nuna goyon baya ga gwamnatin Syria a yakin da take yi da 'yan ta'adda, lamarin da ya fusata Amurka da Saudiyya, inda kwana biyu bayan haka Saudiyya ta sanar da yanke taimakon mai da take baiwa Masar, tare da janye jakadanta daga Alkahira.