Ana Murnar Sakin 'Yan Matan Chibok 21
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i12430-ana_murnar_sakin_'yan_matan_chibok_21
Sako 'yan matan Chibok 21 cikin 219 da kungiyar Boko Haram ta sace fiye da shekaru biyu da suka gabata ya zowa mutane bazata tare da rashin bayani akan yadda suka fito.
(last modified 2018-08-22T06:59:05+00:00 )
Oct 14, 2016 02:28 UTC
  • Ana Murnar Sakin 'Yan Matan Chibok 21

Sako 'yan matan Chibok 21 cikin 219 da kungiyar Boko Haram ta sace fiye da shekaru biyu da suka gabata ya zowa mutane bazata tare da rashin bayani akan yadda suka fito.

A ranar 14 ga watan Afirilun shekarar 2014 ne 'yan kungiyar Boko Haram suka bi dare zuwa makarantar sakandare ta 'yan mata dake cen garin Chibok a arewa maso gabashin Najeriya suka sace 'yan makarantar.

Mai baiwa shugaban kasa shawara ta fannin labarai Garba Shehu ne ya fitar da sanarwar inda ya tabbatar da sako wasu daga cikin 'yan matan, kafin daga bisani mataimakin shugaban kasa ya gana dasu a Abuja.

Shi dai labarin sakin 'yan matan su ishirin da daya ya zowa mutane da mamaki saboda babu takamaiman bayani daga hukumomin tsaron kasar.

Bayanan da aka samu dai ye zuwa yanzu sun nuna cewa kungiyar agajin gaggawa ta kasa da kasa wato Red Cross da gwamnatin Swizerland ne suka shiga tsakani wajen sakin 'yan matan.

Wasu rahotannin sun ce sai da gwamnatin kasar ta saki wasu kusoshin kungiyar Boko Haram guda hudu, kafin kungiyar ta yarda ta saki 'yan matan.

Amma gwamnatin kasar ta musanta hakan, a inda ta ce an saki 'yan matan ne sakamakon tattaunawa da ta fara da 'ya'yan kungiyar.

Mataimakin shugaban kasar Yemi Osinbajo, bayan ya gana da 'yan matan ya bayyana cewa sakinsu da babban labari ga kasar,

Mista Osimbajo ya kara da cewa 'yan matan suna cikin koshin lafiya duk da irin yanayin da ake tsare da su tsawan dogon lokaci.

Wasu majiyoyin sun shaidawa manema labarai cewa hudu daga cikin matan sun zo da 'ya 'ya.

Gwamnatin Najeriya dai ta ce tana fatan wannan sabon babi zai taimaka wajen samo sauren 'yan matan 197 da har yanzu suke hannun 'yan boko haram tun cikin watan Afrilu na shekara 2014.

A nata banagre kungiyar Bring Back Our Girls ta bakin shugabar ta,  tayiwa Allah Godiya da Sako 'yan Chibok din.

Hajiya Aisha Yusuf shugabar kungiyar Bring Back Our Girls da suka shiga zaman dirshen tun lokacin da aka sace 'yan matan Chibok ta yiwa Allah godiya bisa ga sako 21 daga cikinsu da fatan sauran ma za'a sakosu.

Hajiya Aisha tace sun yi farin ciki da labarin kamar su zuba ruwa kasa su sha saboda matukar murna.

Tace tun can farko su san gwamnati zata iya kwato 'yan matan kuma gashi hakan ya soma tabbatuwa. Tace idan Allah ya yadda sauran ma za'a dawo dasu.

Fadar shugaban kasa Najeriya dai a watan daya gabata ta sanar da cutura wata tattaunawa data ce ta soma da kungiyar Boko haram, saboda rarabuwa kawuna da aka samu a baya bayan nan a cikin kungiyar ta boko haram.

A bin rikewa dai shi ne kungiyar boko haram ta sha nema ga wgamnatin Najeriya data sake mata wasu 'ya 'yanta idan ana so ta saki 'yan matan.

Wannan kuma ita ce ayar tambayar da dubban jama'a ke azawa kan su na cewa ko gwamnatin ta Najeriya tayi musayar 'yan boko haram da 'yan matan ne Chibok ne ko kuma A'A.

ko mi zata kasance dai lokaci ne zai fayyace haka......