An cimma matsaya kan dumamar yanayi a duniya
Fiye da kasashe 150 suka amince da wata yarjejeniya domin kawar da sinadarin da ke taimakawa wajen kara dumamar yanayi a duniya.
Taron da ya gudana a birnin Kigali na kasar Ruwanda ya bayyana cewa Sinadarin Hydroflurocarbons (HFCs), wanda ake samu a cikin firinji da na'urar sanyaya daki da kuma sinadaran da ake fesawa irin su maganin kashe kwari ko sauro idan suka fashe, suna matukar illa ga muhalli.
Wakilan kasashen sun amince da wani garambawul da aka yi wa yarjejeniyar Montreal, wacce ta bukaci kasashe masu arziki su rage yawan sinadarin HFC zuwa shekarar 2019.Sai dai masu suka sun ce wannan matakin ba zai yi tasiri sosai wajen rage dumamar yanayin
Sakataren wajen Amurka John Kerry, wanda ya jagoranci taron ya ce matakin babban ci gaba ne wajen samun lafiyar duniya, kuma ya ce wannan babban ci gaba ne domin kuwa zai taimakawa kasashe daban-daban wajen inganta muhalli saboda zai sa a rage dumamar yanayi da kimanin rabin digiri.