Harin 'yan tawaye a wani yankin na kasar Demokaradiyar Kwango
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i12487-harin_'yan_tawaye_a_wani_yankin_na_kasar_demokaradiyar_kwango
Jami'an 'yan sandan Demokaradiyar Kwango sun sanar da 'yan tawaye sun kai hari a wani yanki dake tsakiyar kasar.
(last modified 2018-08-22T06:59:05+00:00 )
Oct 15, 2016 07:19 UTC
  • Harin 'yan tawaye a wani yankin na kasar Demokaradiyar Kwango

Jami'an 'yan sandan Demokaradiyar Kwango sun sanar da 'yan tawaye sun kai hari a wani yanki dake tsakiyar kasar.

Jami'an 'yan sandan sun ce a jiya Juma'a 'yan tawayen Kamwina Nsapu sun kai hari yankin Kabeya Kamuanga dake cikin jihar Kasaï-central, inda suka mamaye wasu gine-gine gwamnati, sannan kuma suka kwashi ganima kafin daga bisani su sanya musu wuta.

Wannan hari dai ya biyo bayan kashe mayakan 'yan tawayen na Kamwina Nsapu biyu da kuma kame daya daga cikin su daga jami'an tsaron kasar a ranar Alkhamis din da ta gabata.

Sanarwar ta ce a yayin gumurzu tsakanin Sojojin Kwango da 'yan tawaye a jiya juma'an, Sojoji sun samu nasarar hallaka 14 daga cikin su tare kuma da kame wasu 4 na daban.